Ilimi
Sheikh Daurawa Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hisba

Shugaban Hukumar Hisba na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus da mukaminsa.
Daurawa ya sanar da saukarsa daga shugabancin hukumar ne bayan kalaman gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi na sukar yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta na yaki da badala a jihar.
Daurawa, ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin hukumar, a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar ranar Juma’a.
Kalaman gwamna Abba Gida-Gida, sun yamutsa hazo a jihar, inda wasu ke ganin kalaman nasa a matsayin wata gaba ta goyon bayan masu aikata badala a jihar.
Idan ba a manta ba hukumar Hisba a jihar ta fito da sabon salon yaki da baɗala, inda ta dinga kai samame wurare shakatawa da otal-otal tana kama masu yawon ta-zubar.
Daga bisani Murja ta yi layar bata daga gidan yari, lamarin da ya tayar da kura da haifar da cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta.
Sai dai gwamnatin jihar a wani martani da ta yi, ta hannun Kwamishinan Yada Labaran jihar, Baba Dantiye, ya musanta wannan zargi da ake yi wa gwamnatin.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
