Labarai
Kwamitin Duba Kan Sabon Mafi Karancin Albashi Ya Mika Rahotonsa Ga Gwamnatin Jigawa
Kwamitin da gwamnatin jihar Jigawa ta kafa domin samar da matsaya kan sabon mafi karancin albashi na kasa ya mika rahotonsa ga sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ismaila Ibrahim Dutse ya rabawa bai wa rediyon Najeriya a Dutse.
Kwamitin ya samu jagorancin tsohon shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Mustapha Aminu.
Da yake gabatar da rahoton, Alhaji Mustapha Aminu ya godewa gwamnatin jihar bisa ganin sun cancanci wannan muhimmin aiki.
Da yake karbar rahoton, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya gode wa kwamatin bisa wannan aiki da ya yi.
“A madadin Gwamna Malam Umar Namadi, ina son in gode muku bisa kwazo da jajircewa da kuka nuna wajen gudanar da wannan aiki”. Inji shi.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
