Labarai
Za A Yi Gyaran Cibiyoyin Kiwon Lafiya 144 A Jihar Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran abokan hulda za su fara aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 144 a fadin jihar domin inganta harkar kiwon lafiya.
Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Husaini Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar lafiya ta Yandoton a karamar hukumar Tsafe.
Dakta Yakubu ya ce makasudin ziyarar tasa ita ce duba halin da cibiyar ke ciki, domin inganta kayan aiki, da fadadata.
A cewarsa, aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko zai kasance na hadin gwiwa ne, yana mai jaddada cewa, shirin zai gyara cibiyoyin kiwon lafiya 62, yayin da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Zamfara za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 4, sannan za a gyara cibiyoyi 18 a karkashin aikin mazabu na jihar.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 11 da sauransu.
Dakta Yakubu ya yi gargadin cewa ba za a amince da rashin zuwan ma’aikata ba, yana mai cewa duk wanda ba zai iya bi ba to ya yi murabus, saboda mutane da yawa suna sha’awar shiga aikin gwamnati.
Ya jaddada cewa, daga yanzu duk jami’in da aka samu da sakaci zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta kasar Sulaiman Isah ya fitar, ya mika godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa bangaren kiwon lafiya na jihar sannan ya yabawa kwamishinar lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun bisa jagorancinta.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
