Labarai
Uwargidan Shugaba Tinubu Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Gwamnan Jigawa
Uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu ta kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi bisa rasuwar mahaifiyarsa da dansa.

Sanata Oluremi Tunubu wadda ta kai ziyarar ta’aziyyar a gidan gwamnati dake Dutse, tace ta isa jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan da iyalansa da gwamnati da ma alummar jihar ta’aziyyar rashin da aka yi.

Kazalika, ta yi addu’ar Allah ya ji kansu ya kuma bai wa gwamnan da iyalansa hakurin jure babban rashin.

A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yi godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma mai dakin sa bisa wannan karamci da kauna da kuma addu’o’in da suka gudanar ga mamatan.

Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya aiko mana da rahoton cewar, Senata Oluremi Tinubu ta samu rakiyar uwar gidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Kashim Shettima da mai dakin shugaban majalisar wakilai ta kasa da dai sauransu.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
