Connect with us

Labarai

Za A Yi Gyaran Cibiyoyin Kiwon Lafiya 144 A Jihar Zamfara

Published

on

 

Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran abokan hulda za su fara aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 144 a fadin jihar domin inganta harkar kiwon lafiya.

Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Husaini Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar lafiya  ta Yandoton a karamar hukumar Tsafe.

Dakta Yakubu ya ce makasudin ziyarar tasa ita ce duba halin da cibiyar ke ciki, domin inganta kayan aiki, da fadadata.

A cewarsa, aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko zai kasance na hadin gwiwa ne, yana mai jaddada cewa, shirin  zai gyara cibiyoyin kiwon lafiya 62, yayin da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Zamfara za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 4, sannan za a gyara cibiyoyi 18 a karkashin aikin mazabu na jihar.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 11 da sauransu.

Dakta Yakubu ya yi gargadin cewa ba za a amince da rashin zuwan ma’aikata ba, yana mai cewa duk wanda ba zai iya bi ba to ya yi murabus, saboda mutane da yawa suna sha’awar shiga aikin gwamnati.

Ya jaddada cewa, daga yanzu duk jami’in da aka samu da sakaci zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta kasar Sulaiman Isah ya fitar, ya mika godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa bangaren kiwon lafiya na jihar sannan ya yabawa kwamishinar lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun bisa jagorancinta.

 

Daga Aminu Dalhatu

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara