Connect with us

Labarai

NDLEA Ta Kama Sama Da Tan 2 Na Miyagun Kwayoyi Da Mutane 929 A Jihar Kwara

Published

on

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Kwara, ta kama tan 2 da digo 6 na miyagun kwayoyi, tare da kama mutane 929 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban wannan shekara.

Kwamandar hukumar ta NDLEA a jihar Kwara, Fatima Popoola ce ta bayyana hakan yayin da take yi wa manema labarai karin haske kan nasarorin da hukumar ta samu a Ilori.

Ta ce daga cikin wadanda ake zargin 839 maza ne yayin da 90 kuma mata ne.

Misis Popoola ta ce magungunan da aka gano sun hada da, tabar wiwi da kwayar Tramadol,  da diazapam, da  methamphetamine, da maganin tari na ruwa da hodar ibilis da sauransu.

Ta ce tabar wiwi da ke kan gaba a jerin kwayoyin ta kai nauyin kilogiram miliyan daya da rabi.

Ta yi nuni da cewa, yayin wani aikin hadin gwiwa da hukumar ta yi cikin gaggawa, ta kama masu shaye-shaye 185, wadanda aka fadakar da su illar shaye-shaye, tare da ba su shawarwari, aka kuma maida su ga iyalansu.

Misis Popoola ta ci gaba da cewa, hukumar  tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, ta fara aiwatar da shirin gwajin magunguna kan sabbin dalibai 261 na jami’ar jihar Kwara.

Kwamandar hukumar ta NDLEA ta yabawa kokarin gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro bisa tallafawa ayyukansu.

Ta shawarci iyaye da su kasance masu sa ido kan al’amuran  ‘ya’yansu don kaucewa tu’ammali da miyagun  mutane.

Misis Popoola ta bukaci gwamnatin jihar da ta taimaka wa hukumar da karin motocin aiki tare da kammala ginin cibiyar gyaran dabi’u domin saukaka ayyukansu.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka wa hukumar da bayanai kan ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi domin samun nasara.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara