Connect with us

Labarai

Mahajjata Sun Yabawa Gwamnatin Borno Da Hukumar Alhazai Bisa Basu Abinci Mai Inganci

Published

on

Alhazan Jihar Borno  sun yabawa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da gwamnatin jihar Borno bisa kyakkyawan tsarin shirin ciyarwa  a  Makka da Madina.

Alhazan da a halin yanzu suke shirin fara aikin Hajji a ranar Juma’a ta makon gobe, sun bayyana gamsuwarsu da inganci da wadataccen abinci da ake basu a kullum.

Wakilinmu Dauda Iliya wanda yanzu haka yake a garin Makka ya ruwaito cewa Alhazai 1,646 daga cikin 1,815 daga jihar sun kammala zamansu a Madina bayan sun yi ziyara a muhimman wurare.

Daya daga cikin mahajjatan  Hajia Fatima Usman ta ce ana basu abincin  mai gina jiki kuma irin wanda suka saba da shi.

“Abincin da muke samu tun daga Madina zuwa nan Makka yana da kyau kwarai da gaske, muna jin dadin yadda ake bamu abincinmu na gargajiya da muka saba da shi, muna godiya ga Hukumar NAHCON da Gwamnatin Jihar Borno da suka tabbatar mana da samun wadataccen abinci a wannan lokacin.” in ji Hajiya Fatima.

Wani Alhaji mai suna Malam Abba Kyari, ya yabawa jami’an kwamitin ciyar da abinci da masu ba da abinci bisa kwarewa da kuma kula da Alhazai.

Kyari ya ce “Ma’aikatan da ke kula da abinci suna matukar bibiyar bukatunmu da korafe-korafenmu, idan akwai. Suna tabbatar da cewa an ba mu abinci a kan lokaci“.

Shugaban kwamitin ciyarwa  na tawagar Amirul Hajj Dr Ibrahim Adam ya bayyana jin dadinsa bisa yabon da Alhazan  ke yi, yana mai cewa hakan ya nuna irin jajircewar da gwamnatin jihar ta yi na kyautata rayuwar jami’ar ta da suke gudanar da aikin Hajjin.

Dangane da korafin da wasu maniyyatan ke yi na rasa abincin, Dr Ibrahim ya ce kwamitin ya bukaci masu kula da abincin da su kara samar da wadataccen abincin a lokacin karin kumallo da kuma abincin dare domin tabbatar da cewa  kowa ya samu.

“Abin da muka sa a gaba shi ne tabbatar da kula da mahajjatan mu a yayin wannan tafiya ta ibada. Yabo daga alhazan Borno ya nuna cewa muna kan turbar da ta dace, kuma za mu ci gaba da hada hannu da NAHCON wajen tabbatar da wannan tsari,” in ji Dokta Ibrahim.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana sa ran za a yi jigilar alhazan jihar Borno na karshe a kasa mai tsarki nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Dauda Iliya

Labarai

Labarai14 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai17 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara