Ilimi
Unimaid Ta Karbi Bakuncin Taro Karo Na Farko Akan Rashin Tsaro
An bude taron kwanaki biyu na kasa da kasa kan matsalar tsaro da sake tsugunar da jama’a da sake gina kasar a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Taron mai taken “Rashin tsaro, Sake Ginawa, Gyara da Matsugunni a Yankin Tafkin Chadi” wanda Tsangayar Nazarin Tarihi da Dabarun mulkin na Jami’ar Maiduguri ne suka shirya, wanda ya samu halartar mahalarta daga ciki da wajen kasar nan.
A nasa jawabin tsohon babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya jaddada cewa akwai bukatar Najeriya ta mai da hankali sosai kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel sakamakon rashin zaman lafiya da yankin ke fuskanta.
Janar Buratai ya ba da shawarar yin garambawul ga ‘yan sandan Najeriya a fannonin fasaha, horarwa, kwarewa da kuma nagarta don tunkarar kalubalen tsaro da ke kunno kai a yankin.
Ya kuma yi kira da a maido da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi domin tabbatar da ci gaba mai dorewa a matakin farko.
Buratai ya kara da cewa, “Bawa kananan hukumomi damar daukar nauyin ayyukansu na ci gaba yana da matukar muhimmanci wajen samar da dorewar zaman lafiya da dorewar yankin, wanda a karshe zai kai ga samar da al’umma mai wadata da daidaito.” Inji Buratai.
Shugaban Jami’ar Maiduguri, Farfesa Aliyu Shugaba ya ce maharan sun kai wa makarantar hari, amma duk da haka ta kasance a bude ko da a lokacin da rikici ya barke.
Ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su yi nazari sosai kan abubuwan tarihi kamar rikicin Boko Haram tare da samar da ingantattun hanyoyin da al’umma ke bukata.
“Na yi farin ciki da cewa Tsangayar Nazarin Tarihi da Dabaru tsaro ta shirya wannan taro na farko na kasa da kasa domin jawo hankulan malamai game da rikicin Boko Haram ta fuskar tarihi.” Shugaba yace.
Shugaban Jami’ar Sojojin Najeriya, Farfesa Kyari Mohammed ya yi kira da a samar da tsarin shari’a na kasa don tafiyar da ficewar jama’a tare da sake shigar da masu tayar da kayar baya a cikin al’umma.
Kimanin kasidun ilimi 40 ne za a gabatar da su yayin taron.
Cov/Dauda/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
