Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Gina Sabbin Makarantun Sakandare 50 A Fadin Jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kammala shirye-shiryen bayar da aikin gina makarantun sakandare 50 a fadin jihar.

Gwamnan jihar Malam Uba Sani ne ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da sabuwar babbar sakandare da aka gina a Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, makarantar  ta Rigachikun na daya daga cikin makarantun sakandire guda 62 da aka bada aikin gina su da kuma gyara a rukunin farko na shirin farfado da ilimi da  gwamnatinsa ta sanya a gaba.

A cewarsa, an kammala akasarin ayyukan da aka bada tare da kaddamar da su, yayin da ake gab da kammala sauran.

Uba Sani ya yi nuni da cewa, ko shakka babu sabuwar makarantar sakandaren za ta samar wa dalibai yanayin karatu mai kyau.

Idan za ku iya tunawa lokacin da na kaddamar da harsashin ginin wannan makaranta a ranar 31 ga watan Agustan 2023, na yi alkawarin cewa za a yi gaggawar kammala ta, yau gashi cikin ikon Allah  an cimma gacci”. Inji shi.

A cewarsa, hakan na nuni da gagarumin mataki a kokarin gwamnatinsa na magance daya daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga fannin ilimi.

Hakazalika, Gwamnan ya kuma kai ziyarar gani da ido  cibiyar koyar da sana’o’i da ake ginawa a Rigachikun.

Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai2 days ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara