Labarai
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitin Kwanar Ganduje A Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta rufe tare asibitin Kwanar Ganduje dake unguwar Sharada Karamar Hukumar Kano Municipal.
Babban daraktan hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano Farfesa Salisu Ibrahim ya bayyana hakan a Kano.
Farfesa Salisu wanda ke zaman kwamitin ladabtarwa na hukumar lafiya ta jihar Kano ya ci gaba da cewa an rufe asibitin ne saboda wasu laifuka.
Ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike tsawon watanni hudu domin tabbatar da korafe-korafen da aka samu a kan asibitin.
Babban daraktan ya jaddada cewa kwamitin ya yi taro da dama kan lamarin bayan ya karbi koke-koke har 11 kan asibitin.
Farfesa Salisu ya yi nuni da cewa, an gayyaci mai asibitin wanda kuma ma’aikaci ne a cibiyar Iman Wali Urology Center Dr. Kabiru da ya bayyana a gaban kwamitin a lokuta da dama.
Ya kara da cewa kwamitin ladabtarwa ya bayar da shawarar rufe asibitin Palace daga jerin asibitocin jihar, saboda wasu laifuka da suka saba wa dokar kafa hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu.
“Daga cikin shawarwarin akwai haramtawa Dr Kabir aiki ko aiki a asibitoci masu zaman kansu dake fadin Kano da kuma cire sunan asibitin Palace daga cikin jerin asibitoci masu zaman kansu a jihar”.
Rediyon Najeriya ya ba da rahoton cewa, a cikin Afrilu 2024 PHIMA ta rufe asibitin Sassauka da cibiyar tantance cutar dake unguwar Rimin Kebe Kano bisa wasu laifuka.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
