Kasuwanci
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Dakatar Da Yanka Nama A Mahauta Na Kwanaki 3
Gwamnatin jihar Kwara ta binne duk wani naman dabbobin da ake zargi yana dauke da guba don gujewa sayarwa mutane a kusa da Kwalejin Kolejin Koyon Larabci da Shari’ar Musulunci ta Jihar Kwara (CAILS) da ke Ilorin.
Hakan ya biyo bayan wasu matakan da aka dauka na hana mutane cin naman dabbobin da ake zargin yana dauke da guba a jihar.
A cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar noma da raya karkara, Madam Funke Sokoya ta fitar, ta ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki sun amince da dakatar da ayyukan yanka dabbobi har na tsawon kwanaki uku domin a samu damar yin feshin magani a Mahautar don dakile duk wata cuta da ke gurin.

Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa mummunan lamarin ya faru ne sakamakon kiwo da gurbatacciyar ciyawa da ke kewaye da yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa, ma’aikatar za ta kara sanya ido a sauran Mayanku daban-daban na jihar domin tabbatar da tsaftar muhalli.
A nasa jawabin, Daraktan Kula da Dabbobi, Dokta Olugbon Saliman, ya ce, za a rage yawan Mahauta da ba na gwamnati ba zuwa matakin da ma’aikatar za ta iya sarrafawa.
Ya ce duk wata Mayanka da ba ta bi ka’idojin gwamnati ba game da tsafta, za a rufe ta.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
