Labarai
EU Ta Ƙara Azama Wajen Tallafa Wa Arewacin Najeriya
Wata babbar tawaga ta shugabannin ofisoshin ƙasashen Tarayyar Turai (EU) da mataimakansu ƙarƙashin jagorancin Jakadan EU a Najeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, ta kammala wata ziyara ta kwanaki da dama a Jihar Kano domin ƙarfafa haɗin gwiwa da bunƙasa ayyukan ci gaba a Arewacin Najeriya. Tawagar ta haɗa da wakilan UNICEF, GIZ, Plan International Nigeria, UN-Habitat da sauran abokan hulɗar ci gaba.
A yayin ziyarar, tawagar ta gana da gwamnatin Jihar Kano inda suka tattauna kan bunƙasa birane, samar wa matasa damarmaki, haɗa kan al’umma da kuma ci gaban tattalin arziki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakin Gwamna Murtala Sule Garo ya wakilta, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da aiki tare da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa domin cimma manufofin ci gaba.
Gwamnatin Kano ta kuma gabatar da tsarinta na bunƙasa birane wanda ke da nufin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, ƙarfafa shirin gine-gine da ababen more rayuwa, bunƙasa zaman lafiya da haɗin kai tare da samar da damar tattalin arziki. Ana aiwatar da shirin ne da tallafin fasaha daga UN-Habitat.
Da yake jawabi, Jakada Mignot ya ce ziyarar ta nuna ƙudirin Tarayyar Turai na ci gaba da kasancewa kusa da al’ummomin Arewacin Najeriya. Ya ce hulɗa kai tsaye da jama’a da cibiyoyi na taimakawa wajen ƙarfafa haɗin gwiwar da ke kawo ci gaba mai anfani ga kowa.
Daraktan GIZ a Najeriya da ECOWAS, Markus Wagner, ya bayyana cewa zuba jari ga matasa da mata yana da muhimmanci wajen gina al’umma masu juriya da ci gaba. Ya ce shirye-shiryen koyar da sana’o’i da tallafa wa kasuwanci na samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
A Jami’ar Bayero da ke Kano, tawagar ta tattauna da ɗalibai kan rawar da matasa za su taka wajen samar da mafita ga matsalolin al’umma. Tattaunawar ta nuna muhimmancin sauraron ra’ayoyin matasa da ba su damar bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.
Tawagar ta kuma ziyarci shirye-shiryen ilimi da UNICEF da Plan International ke tallafawa, ciki har da shirin ilimi na gaggawa da cibiyar ilimin Alƙur’ani. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta ce saka hannun jari a ilimi, lafiya da kariyar yara na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawar makoma ga yara masu rauni.
Har ila yau, tawagar ta ziyarci wata cibiyar samar da abincin kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki tare da ganawa da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood.
An kammala ziyarar da halartar taron tattaunawa na Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma kan rage talauci, inda EU da abokan hulɗarta suka sake jaddada aniyarsu ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa ci gaba a Arewacin Najeriya.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
