Labarai
Hajj2026: Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Daga Kasa Mai Tsarki
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta kammala jigilar dukkan Alhazan jihar zuwa Najeriya bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2026.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan isowar rukuni na ƙarshe na Alhazan Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse.
Ya ce an kwaso Alhazan jihar sahu na farko ne ta jirgin Umza Air daga ƙasa mai tsarki, inda suka sauka a Dutse da daren Asabar.
A cewarsa, jirgi na biyu kuma na ƙarshe ya tashi daga Jeddah da yammacin Lahadi ɗauke da jimillar Alhazai 404, ciki har da Amirul Hajji kuma Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi, wasu mambobin kwamitin Hajji na Majalisar Dokokin Jihar, jami’an shiyyoyi da mataimakansu, ma’aikatan lafiya da kuma tawagar kafafen yaɗa labarai.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa jihar ta gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara ba tare da wata matsala ba.
Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kan da ya bai wa hukumar a lokacin gudanar da aikin Hajjin bana.
Wasu daga cikin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya bayan isowarsu Dutse sun gode wa Allah da Ya ba su damar sauke farali a Hajjin bana.
Sun kuma yabawa gwamnatin jihar da Babban Daraktan Hukumar bisa samar musu da abinci sau uku a rana yayin zamansu a Saudiyya.
Haka kuma Alhazan sun nuna gamsuwa da tsarin wa’azi da aka tanadar musu, tare da yaba wa jami’an hukumar kan kulawa da jin daɗin da suka yi musu a Madina da Makkah.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Alhazan sun iso cikin ƙoshin lafiya tare da kayan hannunsu masu nauyin kilo 8 da kuma manyan jakunkunansu masu nauyin kilo 46.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
