Labarai
Al’ummar Auyo Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Gwamna Umar Namadi
Al’ummar Karamar Hukumar Auyo dake Jihar jigawa daga sassa daban-daban sun sake jaddada cikakken goyon baya da mubaya’arsu ga Gwamna Umar Namadi, bisa irin dimbin ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa a yankin da kuma fadin jihar baki daya.
Sun bayyana haka ne lokacin da tawagar al’ummar ta kai ziyara ga Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse.
Tawagar ta kunshi manyan ‘yan siyasa, malamai da masu ilimin boko da ‘yan kasuwa da masu rike da sarautun gargajiya da matasa da mata da sauran bangarori na al’ummar karamar hukumar.

Sun bayyana gamsuwar su da salon jagoranci na Gwamnan da kuma yadda yake tafiyar da harkokin gwamnati bisa gaskiya da adalci.
Da yake magana a madadin tawagar, Alhaji Garba Muhammad Auyo ya bayyana cewa ayyukan raya kasa da gwamnatin Malam Umar Namadi ke aiwatarwa sun kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’umma, musamman a bangarorin ilimi da lafiya da noma da samar da ababen more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin Jama’a.

Yana mai cewar, a tarihi tunda karamar hukumar Auyo take, ba su taba samun wata babbar makaranta ba sai da zuwan Gwamna Namadi.
Kazalika, sun kuma tabbatar wa Gwamnan cewar al’ummar Auyo za su ci gaba da kasancewa masu biyayya da goyon baya ga gwamnatinsa domin ganin an ci gaba da samun ci gaba mai dorewa a jihar Jigawa.

A nasa bangaren, Gwamna Malam Umar Namadi ya gode wa al’ummar Auyo bisa wannan gagarumar ziyara da kuma nuna masa kauna da amincewa.
Namadi, ya jaddada kudirinsa na ci gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani daukacin al’ummar jihar ba tare da nuna bambanci ba.
Ziyarar ta kara nuna irin kyakkyawar alaka da fahimtar juna da ke tsakanin gwamnatin Jigawa da al’ummar Karamar Hukumar Auyo, tare da tabbatar da cewa tafiyar cigaban jihar na samun cikakken goyon bayan Jama’a, inda Tsohon Babban Sakataren, Alhaji Garba Auyo ya chanja sheka daga Jamiyyar PDP zuwa Jamiyyar APC da dukkan magoya bayansa a gidan Gwamnatin Jigawa dake Dutse.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
