Labarai
Jigawa: An Tsaurara Tsaro a Wuraren Karɓar Kayayyakin Alhazai a Dutse
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta tura jami’an tsaro a wuraren karɓar kayayyakin Alhazai da ke Dutse.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan a wata hira da wakilin RediyonNajeriya, Usman Mohammed Zaria, a birnin Makkah.
Ya ce jirgi na farko ya isa filin jirgin sama na Dutse tare da kayan Alhazai.
A cewarsa, jami’an tsaro da aka tura sun haɗa da ‘yan sanda, jami’an shige da fice, kwastam, hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), da kuma ‘yan sa-kai, waɗanda suke a muhimman wurare domin tabbatar da ingantacciyar kulawa da kayayyakin Alhazai.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ƙara da cewa tawagar hukumar da jami’an tsaro za su taimaka wajen tabbatar da tsari wajen karɓo kayayyakin Alhazai cikin kwanciyar hankali.
Ya ce wannan tsari da aka shirya na da nufin kare dukiyar Alhazai tare da hana duk wani shige da fice da bai dace ba wurin kayayyakinsu.
Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa an ba Alhazai tambari (tags) domin gano kayayyakinsu a sansanin Alhazai.
Labbo ya kuma yi kira ga Alhazai da su ba da cikakken haɗin kai ga dukkan jami’an tsaro yayin karɓar kayayyakinsu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa rukuni na farko na Alhazai 484 sun isa filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse, babban birnin jihar, bayan kammala aikin hajjin bana.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
