Labarai
Jihar Jigawa Za Ta Yi Aikin Idanu Kyauta ga Alhazai a Makka
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa ta sanar da kulla haɗin gwiwa da wata gidauniya da ke Makkah a Ƙasar Saudiyya domin samar da ayyukan kula da idanu kyauta ga Alhazan jihar.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a birnin Makkah na Ƙasar Saudiyya.
Ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ci gaba da ƙirƙiro shirye-shirye da tsare-tsaren da za su tallafa wa Alhazai kai tsaye, tare da inganta lafiyarsu a duk tsawon zamansu a ƙasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin hukumar na tabbatar da lafiya da walwalar Alhazan jihar.
Babban Daraktan ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da aka ƙulla tsakanin hukumar da gidauniyar na da nufin samar da cikakkun ayyukan kula da idanu kyauta, ciki har da tiyatar cire hazo (cataract) da kuma ba da magunguna ga dukkan Alhazan jihar.
Wakilin Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa a shekarar 2025, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ƙaddamar da shirin kula da idanu kyauta tare da wani asibiti a Ƙasar Saudiyya domin Alhazan jihar, wanda ya samu gagarumar nasara a birnin Makkah.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
