Labarai
Hajj2026: Alhazan Jigawa na Daga Cikin Mahajjata da Suka Jefa Duwatsu Miliyan 100 a Jamarat
Daga Usman Muhammad Zaria
Jifar Jamarat na ɗaya daga cikin muhimman ibadun Hajji da ake maimaitawa.
Alhazai kan fara jifar Jamaratul Aqaba a ranar Layya, wato 10 ga Zul-Hijja, a matsayin ranar farko ta jifa.
A kwanakin Tashriƙi (Ayyamut-Tashriƙ), Alhazai kan jefi ginshiƙan Jamarat uku da duwatsu guda bakwai-bakwai.
Suna farawa ne daga Jamaratus Sugra (Jamra ƙarama), sannan Jamaratul Wusta (Jamra matsakaiciya), sannan a kammala da Jamaratul Aqaba (Jamra Babba), inda amfani da duwatsu guda bakwai a kowanne.

A bana, sama da Mahajjata miliyan 1 da dubu 700 daga cikin gida da ƙasashen waje ne suka gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Da yake zantawa da Rediyon Najeriya, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yabawa hukumomin Saudiyya bisa yadda suka tsara hanyoyin zirga-zirgar Alhazai cikin tsari da inganci.
Labbo ya kuma yabawa Alhazan Jihar Jigawa bisa nuna ladabi, biyayya da ɗa’a a lokacin zamansu a Mina, Arfa da Muzdalifa.

Wasu daga cikin Alhazan jihar, ciki har da Alhaji Isah Abubakar daga Kazaure da Alhaji Abdullahi Ya’u, sun bayyana cewa ba su fuskanci wata matsala ba yayin gudanar da jifar Jamarat.
Alhazan da suka yi jifa a cikin kwanaki uku sun yi amfani da sama da duwatsu miliyan 83, domin kowane mahajjaci ya yi amfani da duwatsu guda 49. Wadanda suka ci gaba da zama a Mina zuwa ranar huɗu kuma sun yi amfani da duwatsu guda 70 kowannensu.
Wannan na nufin cewa sama da duwatsu miliyan 100 ne aka yi amfani da su a Hajjin shekarar 1447 da ta ƙare a yau Asabar, 30 ga watan Mayun 2026.
Mutane da dama kan yi mamakin abin da ke faruwa da waɗannan miliyoyin duwatsu bayan Alhazai sun kammala jifa kuma suka bar Mina, inda yankin Jamarat ke sake zama babu kowa har zuwa Hajjin shekara mai zuwa.
Amsar wannan tambaya na nuna irin tsare-tsaren kimiyya da tsafta da gwamnatin Saudiyya ta tanada wajen kula da waɗannan duwatsu bayan an yi amfani da su.
Ana fara tattara duwatsun nan take bayan Alhazai sun kammala ibadar jifa a ranakun farko, na biyu da na uku.
Duwatsun kan faɗa ne a tsaye zuwa ƙasa ta cikin ginshiƙan Jamarat da ke matakai huɗu na ginin, inda suke taruwa a wani babban ɗaki da ke ƙasa mai zurfin kusan mita 15.
An kuma tanadi wasu manyan bel-bel masu motsi (conveyor belts) da ke tattara duwatsun domin tace su tare da feshe su da ruwa domin cire ƙura da datti.
Bayan an tsabtace su, ana ɗora duwatsun a cikin motocin dakon kaya domin kai su wuraren ajiya na musamman don ci gaba da sarrafa su bayan kammala aikin Hajji.
A shekarar da ta gabata, hukumomin da abin ya shafa sun samar da fiye da buhuna 90,000 na duwatsu domin amfani wajen jifar Jamarat.
Haka kuma, an rarraba duwatsun a wurare sama da 300 da ke kan hanyoyin da alhazai ke bi a Muzdalifa, baya ga wuraren da ke kusa da gadar Jamarat a Mina.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
