Labarai
2026Hajj: An Raba Manyan Jakunkuna 2 Masu Nauyin Kilogiram 46 ga Kowane Mahajjacin Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa ta bada jakunkunan kaya guda biyu masu nauyin kilo 23 ga kowane Mahajjaci a birnin Makkah, wanda jimillar nauyinsu ya kai kilo 46.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya jaddada cewa ya zama wajibi a bi ƙa’idar nauyin kaya da aka amince da ita, wato kilo 46 ga kowane Alhaji (jakunkuna biyu masu nauyin kilo 23 kowacce) da kuma kilo 8 na jakar hannu.
Ya bayyana cewa hukumar ta tanadi na’urorin auna kaya a dukkan masaukan Alhazai da ke Makkah domin ba su damar duba nauyin kayansu kafin fara aikin jigilar kayayyakinsu.

Ya yi gargaɗin cewa rashin bin ƙa’idar nauyin da aka kayyade na iya janyo tsaiko ga dawowarsu Najeriya bayan kammala aikin Hajji.
Ya ƙara da cewa Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON da hukumomin Saudiyya ba za su lamunci kaya masu nauyin da ya wuce ƙa’ida ba.
Ahmed Labbo ya kuma gargadi Alhazai da su guji ɗaukar abubuwa masu kaifi, bindigar wasa ko ta gaske, abubuwan fashewa, abubuwa masu saurin kamawa da wuta, wuƙaƙe, reza da almakashi a cikin kayansu na hannunsu.

Ya bayyana cewa kowane Alhaji yana da haƙƙin karɓar lita biyar na ruwan Zamzam, wanda tuni aka yi jigilarsa zuwa Najeriya.
A cewarsa, Alhazan da kayansu suka zarce nauyin da aka kayyade za a buƙaci su miƙa kayan ga kamfanonin jigilar kaya da NAHCON ta amince da su.
Labbo ya kuma tabbatar da cewa da zarar Alhazai sun iso Najeriya, za su karɓi manyan jakunkunansu tare da lita biyar na ruwan Zamzam da aka ware musu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
