Labarai
INEC Za Ta yi Zaben Cike Gurbi na Dawakin Kudu/Warawa Ranar 20 ga Watan Yuni
Daga Khadijah Aliyu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta bayyana ranar 20 ga watan Yunin 2026 domin gudanar da zaɓen cike gurbi na kujerar Warawa/Dawakin Kudu a Jihar Kano bayan rasuwar ɗan majalisar wakilai.
Kwamishinan Zabe na Jihar (REC), Zango Abdu, ya ce an riga an fara shirin zaɓen, inda aka kai ziyara domin duba matakin shiri a ƙananan hukumomin Warawa da Dawakin Kudu.
Ya bayyana cewa Warawa na da rumfunan zaɓe 303 da masu rajista 162,445, yayin da Dawakin Kudu ke da rumfunan zaɓe 143 da masu rajista 75,623
INEC ta ce fiye da ma’aikata 2,000 ne za a tura domin gudanar da aikin, tare da haɗin gwiwar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, da jami’an tsaro don tabbatar da zaɓe lami lafiya.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa Kano na kan gaba a rajistar sabbin masu kaɗa ƙuri’a, inda fiye da mutum 210,000 suka yi rajista, kuma sama da 190,000 sun kammala cikakken rajista.
REC ya roƙi ‘yan siyasa da su guji tashin hankali, yana mai cewa ana bukatar zaman lafiya domin sahihin zaɓe mai inganci.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
