Labaran Gida
Rijistar Haihuwa Ta Zamani Ta Ƙara Samun Shaida Ga Yara a Ƙauyukan Kano
A faɗin ƙauyuka da biranen Najeriya, rijistar haihuwa na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da asali, zama ɗan ƙasa, da kuma samun damar amfani da muhimman ayyukan gwamnati.
Sai dai har yanzu, da dama daga cikin yara—musamman a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa—ba sa samun wannan muhimmiyar dama. Rashin isassun cibiyoyin rajista, ƙarancin kayan aiki, da kuma dogaro da tsarin rubuce-rubuce na hannu na ci gaba da kawo cikas wajen cikakken rajistar haihuwa.
A baya, tsarin rijistar haihuwa a Najeriya yana amfani da takardu ne kawai ƙarƙashin Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC), inda ake gudanar da rajista a ofisoshin ƙananan hukumomi. Wannan tsarin yana tafiya a hankali, ba shi da tsari mai ƙarfi, kuma yana fuskantar matsalolin ruɗani, ɓacewar bayanai, da jinkirin fitar da takardun haihuwa.
Domin magance wannan matsala, Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar UNICEF sun ƙaddamar da tsarin rajistar haihuwa ta zamani wato Electronic Birth Registration (eBR), wanda ke amfani da fasahar zamani wajen sauƙaƙa da inganta aikin rajista a faɗin ƙasar.
Wannan shiri ya haifar da haɗin gwiwa tsakanin NPC, Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), ALGON, Banksforte Technologies Limited, da UNICEF. Haɗin gwiwar ne ya samar da manhajar Vital Registration (VitalReg), wacce ke taimaka wa rajistar haihuwa tare da haɗa ta da tsarin lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN).
Da tallafin Gwamnatin Netherlands, ana aiwatar da shirin “Accelerating Birth Registration and Leave No Child Behind in Nigeria 2026” a jihar Kano, domin ƙara wayar da kai da kuma ƙarfafa tsarin rajistar haihuwa a matakin ƙasa.
A cikin wannan shiri, an mayar da hankali kan kai ayyukan rajista har zuwa ƙauyuka, tare da haɗa shi da gangamin wayar da kai ga al’umma, musamman a yankunan da ke da ƙarancin samun sabis.
A unguwar Mainika Babban Gida da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, an ga yadda jama’a suka fito da yawa domin yin rajistar haihuwar ‘ya’yansu a gidan shugaban unguwa.
Wata mahaifiya mai shekara 35, Hadiza Lawan, ta ce ta zo da ɗanta mai watanni 12 domin yi masa rajista bayan da ta fahimci muhimmancin hakan.
Ta ce wayar da kai da aka yi a cikin al’umma ne ya sa ta gane cewa rashin rajistar haihuwa na iya hana yaro samun ilimi, kiwon lafiya, kariya ta zamantakewa da sauran dama a nan gaba.
“Mijina ne ya ƙarfafa ni in yi wa dukkan ‘ya’yana rajista. Na gabatar da katin shaidar ɗan ƙasa na mijina da kuma katin rigakafin Yusuf. Ba na so ɗana ya rasa dama a gaba. Har ma an sanar da mu cewa rajistar haihuwa na taimakawa wajen samun fasfo da biza,” in ji ta.
Wata uwa mai ‘ya’ya shida, Maryam Sagiru, ta bayyana rajistar haihuwa a matsayin wata hanya ta kare haƙƙin yara da makomarsu.
Ta ce tsarin dijital zai taimaka wa iyaye wajen guje wa matsalolin da ke shafar shigar yara makaranta da tafiya da samun ayyukan gwamnati.
Shugaban unguwar Mainika Babban Gida, Hayatu Sambo, ya ce sarakunan gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai ta hanyar tarurruka da masu sanarwa da kuma haɗin gwiwa da malamai da shugabannin al’umma.
Ya kuma yaba wa UNICEF da hukumomin gwamnati bisa kawo shirin kusa da al’umma, amma ya nuna damuwa kan matsalar tsaro da ke hana wasu yankuna shiga irin waɗannan shirye-shirye.
Wakilin ALGON a Gwarzo LGA, Rabiu, ya ce an riga an yi wa fiye da yara 3,600 rajista daga cikin 10,000 da aka sa a gaba a yankin.
Ya kuma bayyana cewa kowace unguwa tana da wurin yin rajista, inda ake sa ran iyaye su kammala aikin tare da karɓar takardun haihuwa.
Haka kuma, wakilin NPC, Bashir Aminu, ya ce tsarin eBR ya inganta yadda ake adana bayanai da kuma saurin bayar da takardun haihuwa.
Ya ƙara da cewa tsarin yana haɗa rajistar haihuwa da ayyukan kiwon lafiya kamar rigakafi, tare da kai sabis har zuwa matakin unguwa domin sauƙaƙa wa jama’a.
Yayin da Najeriya ke ƙoƙarin rufe gibin da ke hana yara samun shaidar asali, masu ruwa da tsaki sun ce ƙarfafa wayar da kai da inganta fasahar dijital da kuma kai ayyuka kusa da jama’a zai taimaka wajen tabbatar da cewa babu yaro da aka bari a baya.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
