Labarai
Kafafen Yada Labarai Sun Yi Kira Da A Kare Muryar Ɗan Adam Daga Shafar Fasahar AI
n yi kira ga masu aikin kafafen yada labarai da su riƙa kare martabar ɗan Adam a yayin da fasahar Artificial Intelligence (AI) ke ƙara yaɗuwa cikin sauri, domin gudun kada fasaha ta maye gurbin muhimmancin muryar ɗan Adam da sadarwa kai-tsaye tsakanin mutane.
Bishop na Cocin Katolika ta Ilorin, Most Reverend Anselm Pendo Lawani, ne ya yi wannan kira yayin bikin Ranar Sadarwa ta Duniya na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Ilorin.
Ya bayyana cewa masu aikin sadarwa suna da muhimmiyar rawa a matsayin abokan aikin Kristi, wanda ya kira “Mafi Girman Mai Sadarwa.”
“Mu masu sadarwa ne kuma mabiyan Kristi, wanda shi ne Mafi Girman Mai Sadarwa. Ya umurce mu da mu ci gaba da aikin yaɗa Bishara ga kowa. Don haka muna bin sawunsa,” in ji shi.
Lawani ya ce ci gaban fasaha tun daga juyin masana’antu har zuwa zamanin AI an tsara su ne domin su inganta rayuwar ɗan Adam, ba domin su maye gurbin ɗan Adam ba.
A cewarsa, duk wata sabuwar fasaha ta baya ta yi wa ɗan Adam hidima ne, ba ta rage masa daraja ba, don haka dole ne AI ma ta kasance mai hidima ga ɗan Adam.
Ya jaddada buƙatar kare abin da ya kira “tsarkin asalin ɗan Adam,” inda ya ce kowane mutum na da darajar da ba za a iya maye gurbinta ba.
“Idan muka kare fuskokinmu da muryoyinmu, to muna kare kanmu ne. Ba mu wata halitta da ta dogara da ƙididdigar sinadarai kawai ba. Kowane mutum na da manufa ta musamman da ke bayyana ta hanyar sadarwa da wasu,” in ji shi.
Ya kuma yi gargaɗi cewa yawan dogaro da AI na iya raunana aikin jarida tare da ƙara yaɗuwar labaran ƙarya, cin zarafin mutane ta yanar gizo, damfara da kuma sarrafa bayanai ta hanyar da ba ta dace ba.
Lawani ya buƙaci a ƙara wayar da kai kan amfani da fasaha da kuma ƙarfafa horon ɗabi’a ga ‘yan jarida, yana mai jaddada cewa dole fasaha ta kasance ƙarƙashin jagorancin ƙa’idojin ɗan Adam.
“Muna buƙatar a sake dawo da fuskoki da muryoyi wajen magana da mutane. Ya kamata mu riƙa ganin sadarwa a matsayin tushen gaskiyar ɗan Adam, wacce duk wani ci gaban fasaha ya kamata ya dogara da ita,” in ji shi.
Ya kuma goyi bayan gargaɗin da Fafaroma ya yi, inda ya nuna damuwa kan barin tunanin ɗan Adam a hannun na’urori.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
