Labarai
NHRC Ta Bukaci A Dauki Matakin Haɗin Kai Wajen Kare Haƙƙin Dan Adam A Zamfara
Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta yi kira da a ɗauki matakin haɗin kai wajen kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya, inda ta bayyana cewa ba ya kamata a bar aikin kare haƙƙin ga hukumomin tsaro kaɗai ba.
Ko’odinetan NHRC na jihar Zamfara, Abdullahi Abubakar ne ya bayyana haka a wani taron shawarwari kan shirin shekaru biyar na bunƙasa haƙƙin jama’a na zamantakewa da siyasa, wanda aka gudanar a birnin Gusau.
Ya ce matakin aiwatar da shirin ƙasa na 2026, wanda ke cikin Tsarin Aiki na Ƙasa (NAP) na shekarar 2023 zuwa 2028, an tsara shi ne domin taimaka wa jama’a su ƙara fahimtar haƙƙinsu da kuma nauyin da ke kansu.
Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa hukumar NHRC ta shirya wannan taro ne domin ƙara wayar da kai da kuma ƙarfafa aiwatar da shirin a matakin jiha.
Ya ce taron ya haɗa jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula, ‘yan jarida, sarakunan gargajiya da kuma ƙungiyoyin al’umma domin tattauna hanyoyin inganta kare haƙƙin ɗan Adam da tabbatar da zaman lafiya.
A cewarsa, muhimman batutuwan da aka tattauna sun haɗa da rashin tsaro, cin zarafin iko, kare haƙƙin yara, wariyar jinsi, samun adalci, wayar da kai, da kuma buƙatar ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomi.
Ya kuma ce har yanzu ana fuskantar ƙalubale wajen aiwatar da shirin, ciki har da rashin aikin yi, rashin tsaro, rashawa, da kuma rashin daidaiton rabon ayyukan jin daɗin jama’a.
Ko’odinetan ya ƙara da cewa hukumar na da alhakin sa ido kan ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs) domin tabbatar da cewa suna bin ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam.
A nasa jawabin, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Zamfara, Ahmad Mohammed Bello, ya ce rundunar ‘yan sanda na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kare haƙƙin jama’a.
Ya bayyana cewa rundunar ta kafa sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe domin duba dukkan zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam.
Wakilan da suka halarci taron sun yi kira da a ƙara inganta aiwatar da dokoki, a ƙara wayar da kai ga jama’a, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomi domin inganta kare haƙƙin ɗan Adam a Zamfara da Najeriya baki ɗaya.
Sun kuma ba da shawarar ƙarfafa haɗin gwiwa, faɗaɗa yaƙin wayar da kai, da kuma inganta aiwatar da manufofin kare haƙƙin ɗan Adam.
COV/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
