Kasuwanci
NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Biya Diyya Ga Wasu ‘Yan Nijeriya
Hukumar kula da kamfanonin Sadarwa ta kasa ta umurci kamfanonin sadarwar wayar hannu a Najeriya da su biya diyya ga kwastomomin da suka fuskanci matsalar rashin ingancin sadarwa a yankunan da kamfanonin suka kasa cika ka’idojin ingancin sadarwa da aka gindaya.
A cikin wata sanarwa da shugabar sashen hulɗa da jama’a ta hukumar, Nnenna Ukoha ta sanya wa hannu, an ce wannan umarni ya wajabta wa kamfanonin sadarwar su biya diyya kai tsaye ga masu amfani idan an samu gazawa wajen cika ma’aunin ingancin sadarwa.
Hukumar ta bayyana cewa za a bayar da wannan diyya ne ta hanyar ƙarin kuɗin kira, wanda za a ƙididdige bisa la’akari da yadda masu amfani ke kashe kuɗi a matsakaici da kuma kasancewarsu a ƙananan hukumomin da aka samu matsalar sadarwar a cikin wani takamaiman lokaci.
NCC ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na kare haƙƙin masu amfani da sadarwa tare da tabbatar da cewa ba su ne za su ɗauki nauyin matsalolin da suka samo asali daga gazawar kamfanonin sadarwa ba.
A cewar hukumar, harkokin sadarwa suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki, hulɗar jama’a da kuma samun damar cin gajiyar fasahar zamani, kuma rashin ingancin sadarwa na yin illa ga ayyukan yau da kullum, kasuwanci da kuma amincewar jama’a ga tsarin sadarwa.
Hukumar ta ƙara da cewa duk da cewa tara na daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen hukunta kamfanonin da suka gaza samar da ingantaccen sadarwa, sabon matakin ya fi mayar da hankali ne kan kare muradun masu amfani tare da ƙara ɗora alhakin inganta sadarwa kan kamfanonin sadarwa.
Baya ga wannan umarni na biyan diyya, NCC ta kuma umurci kamfanonin dake kula da turakun sadarwa da ke da alhakin kula da muhimman kayan aikin sadarwa kamar turakun da su zuba jari wajen inganta kayan aikin sadarwa ta hanyar amfani da kuɗaɗen tarar da aka ci su, tare da wasu ƙarin matakan tara da hukumar za ta ɗauka.
NCC ta jaddada cewa dole ne kamfanonin sadarwa su ci gaba da zuba jari wajen ƙarfafa tsarin sadarwa, faɗaɗa ƙarfin aiki da inganta kayayyakin more rayuwa domin biyan buƙatun da ke ƙaruwa a fannin sadarwa.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da amfani da matakan sa ido da doka domin tabbatar da adalci, gaskiya da ɗora alhaki a fannin sadarwa, tare da tabbatar da cewa duk masu amfani da layukan sadarwa suna samun ingantaccen sadarwa da ya dace da bunƙasar tattalin arzikin dijital na Najeriya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
