Labarai
Ukraine Na Zargin Isra’ila Da Sayen ”Hatsin Sata”
Ukraine ta gayyaci jakadan Isra’ila a ƙasar, bayan da Kyiv ta zargi Isra’ilar da sayen abin da ta kira hatsin sata daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.
Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce irin wannan sayayya na kawo cikas ga alaƙa mai kyau da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce jirgin ruwan dakon kaya na biyu ya isa Haifa, bayan na farkon ya kai hatsi yakin.
Ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Sa’ar ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa zargi ba shaida bane, inda ya ja hankalinsu kan gudanar da hulɗar diflomasiyya ta intanet ko kafafen yaɗa labarai.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
