Labarai
Shugabar Ma’aikatan Kano Ta Sha Alwashin Sauya Fasalin Aikin Gwamnati
Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta jaddada kudirinta na aiwatar da gyare-gyare a ma’aikatar gwamnati domin inganta aiki yadda ya kamata.
Ta bayyana haka ne lokacin da ta karɓi baƙuncin tsofaffin ɗaliban ajin 1992/93 na Kwalejin CASRS Kano, waɗanda suka kai mata ziyarar taya murna bisa naɗin da aka yi mata.
Hajiya Bilkisu ta ce za ta rungumi tsarin bada dama ga kowa, domin ƙarfafa gaskiya, haɗin kai da kuma karɓar shawarwari masu amfani wajen bunƙasa aikin gwamnati a jihar.
Ta kuma yaba wa takwarorinta na tsohon ajin bisa irin nasarorin da suka samu a fannoni daban-daban, inda ta ce hakan alama ce ta ingantaccen tarbiyya da ilimin da suka samu tun daga makaranta.
A madadin tawagar, Malam Lawan Ado ya ce sun kai ziyarar ne domin taya ta murna tare da yi mata addu’ar samun nasara a sabon muƙaminta.
Shi ma shugaban NIPR na Jihar Kano, Aliyu Yusuf, ya yabawa shugabancinta, yana mai cewa jajircewarta da ƙwazonta sun sa take ci gaba da samun karɓuwa a aikin gwamnati.
Shugabar Ma’aikatan Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta tabbatar da aniyarta na kawo sauye-sauye a ma’aikatan gwamnati ta hanyar shugabanci na gari dake sauraron kowa, yayin da tsofaffin abokan karatunta suka kai mata ziyarar taya murna da yi mata addu’ar nasara.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
