Connect with us

Kasuwanci

Tinubu Ya Nada Hukumar Gudanarwa Ta NCC Da Sauran su

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kundin tsarin mulki na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da asusun samar da ayukka na kasa da kasa (USPF), dukkanin su a karkashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani.

 

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce an nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC, yayin da Dr. Aminu Waida ya ci gaba da zama mataimakin shugaban zartarwa/Babban jami’in gudanarwa, mukamin da aka nada shi a watan Oktoban 2023 kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Nuwamba na wannan shekarar.

 

A baya Olorunnimbe ya yi aiki a hukumar kula da ayyukan yi na jihar Legas (LSETF), inda ya jagoranci kwamitin masu ruwa da tsaki da gudanar da mulki tare da jagorantar shirye-shiryen samar da ayyukan yi da samar da kasuwanci ga matasa.

 

Sauran mambobin hukumar NCC sun hada da Abraham Oshidami (Kwamishina, Ayukkan Fasaha), Rimini Makama (Kwamishiniyar Gudanarwa), Hajia Maryam Bayi (Kwamishinar kula da ma’aikata), Col. Abdulwahab Lawal (Rtd), Sanata Lekan Mustafa, Chris Okorie, Gimbiya Oforitsenere Emiko, da Sakataren Hukumar.

 

 

Ga USPF, Dokta Bosun Tijani, Ministan Sadarwa, Ƙirƙiri da Tattalin Arziki na Zamani, zai zama shugaba. Olorunnimbe kuma an nada mataimakin shugaba.

 

Sauran mambobin sun hada da Oshidami, Makama, Aliyu Edogi Aliyu (wakilin FMCIDE), Joseph B. Faluyi (Ma’aikatar Kudi ta Tarayya), Auwal Mohammed (Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta Tarayya), Uzoma Dozie, Peter Bankole, Abayomi Anthony Okanlawon, Gafar Oluwasegun Quadri, da Sakataren USPF.

 

PR/Bello Wakili

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara