Labarai
‘Yan Sandan Kwara Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashi Da Makami Da Kuma Kungiyoyin Asiri
Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta kama wasu da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma kasancewa mambobin kungiyar asiri da ke addabar yankin Amoyo a Ilorin.
A cikin wata sanarwa, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce kamen wani babban ci gaba ne a kokarin da rundunar ke yi na yaki da miyagun laifuka.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun rahoto a ofishin ’yan sanda na Amoyo kan wani hari da aka kai a mahadar Kabba Kajola, jami’an tsaro suka gudanar da bincike cikin gaggawa wanda ya kai ga cafke Abdulazeez Isiaq, wanda aka fi sani da Pumpin, da kuma Rilwan Mohammed, yayin da ake ci gaba da neman wani da ake zargi wanda har yanzu bai shiga hannu ba.
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun kai hari ga wasu mutane, inda suka tilasta musu shiga wani ginin da ba a kammala ba wanda suke amfani da shi a matsayin maboya, sannan suka yi musu barazanar kisa tare da kwace musu kayayyakinsu masu daraja.
Sanarwar ta kara da cewa an samu kwato wata bindiga kirar gida da kuma daya daga cikin wayoyin da aka kwace daga hannun wadanda ake zargin, inda kuma suka amsa laifin da ake zarginsu da shi.
Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Aliyu Muhammad Rabi’u/Kwara
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
