Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Tantance Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamna
Daga Khadijah Aliyu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 12 domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna.
Hakan ya biyo bayan karanta wasiƙa daga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya buƙaci majalisar ta tantance tare da amincewa da nadin.
Shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore ne ya karanta wasikar yayin zaman majalisar.
Ya ce gwamnan na neman amincewar majalisa ne domin nada Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna bisa tanadin Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.
Buƙatar ta biyo bayan murabus na son rai da tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi a ranar 27 ga watan Maris, 2026, wanda ya haifar da gurbi a kujerar.
A cikin wasiƙar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa nadin Garo ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da aka yi da shugabannin siyasa, da na addini da shugabannin al’umma a faɗin jihar.
Ya bayyana wanda aka nada a matsayin gogaggen jami’in gwamnati mai ƙwarewa, tare da gogewa a matakin ƙasa da na jiha.
Garo ya taɓa rike mukamai da suka haɗa da Mai Baiwa Gwamna Shawara kan harkokin jam’iyyun siyasa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Kano, da kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta.
Gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwa cewa gogewa, biyayya da fahimtar yanayin siyasa da gudanarwa da Garo ke da su za su taimaka wajen inganta shugabanci da samar da ribar dimokuraɗiyya a jihar.
Ya kuma buƙaci majalisar ta gaggauta duba wannan nadi tare da ba da amincewar da doka ta tanada.
Bayan tattaunawa, majalisar ta kafa kwamitin mutum 12 na tantancewar wanda Mataimakin Shugaban Majalisa, Muhammad Bello Butu Butu, ke jagoranta.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Shugaban Masu Rinƙaye, Babban Mai Tsawatarwa, Mataimakin Shugaban Masu Rinƙaye, Mai Tsawatarwa na Masu Rinƙaye, da ’yan majalisar da ke wakiltar Fagge, Sumaila, Warawa, Dawakin Kudu da Tudun Wada.
Mataimakin Magatakarda na Majalisa ne zai kasance sakataren kwamitin.
An ba kwamitin wa’adin gabatar da rahotonsa ga majalisa ranar Litinin.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
