Connect with us

Labarai

Mataimakin Sakataren APC na Kasa ya bayyana aniyarsa ta takarar Sanatan Nasarawa ta Yamma

Published

on

Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Abdulkareem Abubakar Kana, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Nasarawa ta Yamma a zaɓen 2027.

Farfesa Kana ya sanar da haka ne a Lafiya, inda ya jagoranci magoya bayansa zuwa sakatariyar APC ta jihar domin sanar da shugabannin jam’iyyar burinsa.

Ya ce ya yanke shawarar tsayawa takarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin Keffi da Karu da Kokona da Nasarawa da kuma Toto.

Kana ya ce burinsa ba na kansa ba ne, illa amsa kiran al’umma domin samar da wakilci nagari a majalisar dattawa.

Har ila yau, ya yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Sule, bisa goyon bayan da ya nuna wa Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda yake so ya gaje shi a 2027, yana mai alƙawarin yin aiki domin tabbatar da nasarar sa.

A nasa ɓangaren, shugaban APC na jihar Nasarawa, Dakta Aliyu Bello, ya yabawa Farfesa Kana bisa bin tsarin jam’iyya wajen bayyana aniyarsa, tare da buƙatar ya gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali da nuna ƙwarewa.

Aliyu Muraki/Lafiya

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara