Connect with us

Kasuwanci

Shugabannin siyasar Enugu sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu a 2027

Published

on

Wasu manyan shugabannin siyasa daga jihar Enugu sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Shugabannin, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Peter Mbah, sun bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya gode wa shugabannin bisa goyon bayan da suka nuna masa, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun fara haifar da ci gaba a fannoni kamar lafiya da ilimi da ababen more rayuwa.

Ya kuma yaba wa gwamna Mbah bisa yadda yake tafiyar da harkokin tsaro da ci gaban jihar Enugu, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da jihar domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

A nasa jawabin, gwamna Peter Mbah ya ce sun je Abuja ne domin nuna godiya ga shugaban ƙasa bisa tallafin da gwamnatin tarayya ke bai wa jihar Enugu, tare da tabbatar da cewa al’ummar jihar za su mara masa baya a zaɓen 2027.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, ya ce ci gaban da ake gani a Enugu ya samu ne sakamakon haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya, yana mai tabbatar da cewa jihar za ta goyi bayan Tinubu a wa’adi na biyu.

Bello Wakili/Abuja

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara