Labarai
Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin kakaba doka kan masu karya ka’idojin hanya
Gwamnatin jihar Zamfara ta umurci hukumomin tsaro da su tsaurara matakai kan masu karya dokokin hanya a faɗin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayar da umarnin yayin karɓar rahoto kan laifukan karya dokokin hanya a Gusau.
Ya ce halayen wasu masu amfani da hanya na ci gaba da jefa rayukan jama’a cikin haɗari, don haka ya umurci jami’an tsaro su kamo tare da gurfanar da masu laifi ba tare da nuna bambanci ba.
Haka kuma, ya gargadi jami’an da su guji karɓar cin hanci yayin aiwatar da wannan aiki, yana mai cewa duk wanda aka samu da sakaci ko karya doka ba za a lamunta masa ba.
Gwamnatin ta kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin dokokin hanya domin rage yawan haɗurran mota.
Daga cikin shawarwarin kwamitin da aka kafa har da samar da rundunar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin aiki tare da kotun laifukan hanya ta jihar.
A cikin makon da ya gabata kaɗai, kotun laifukan hanya ta samu nasarar hukunta kimanin masu karya dokokin hanya 270 a faɗin jihar.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
