Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta nemi a sake duba Shirin daukar malamai na SUBEB
Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan aikin daukar malamai da hukumar SUBEB ta jihar ta yi, saboda zargin samun kura-kurai a tsarin.
Bukatar hakan ta fito ne daga wani kudiri na gaggawa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Dambatta, Murtala Musa, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar, Jibril Falgore, ya jagoranta.
Dan majalisar ya ce an samu matsaloli a tsarin daukar aikin, musamman wajen tura wasu wuraren da suka yi nisa da inda suke zaune.
Ya kuma bayyana cewa shawarwarin da kwamitin majalisar ya bayar tun farko ba a aiwatar da su ba, duk da an tattauna da shugaban SUBEB.
Majalisar ta ce ta samu korafe-korafe da dama daga sassa daban-daban na jihar, wanda ya sa ta kira shugaban SUBEB domin ya bayyana yadda aka gudanar da aikin.
Mataimakin kakakin majalisar ya ce ba sa adawa da tantancewa, amma suna bukatar a tabbatar da gaskiya da bin ka’ida wajen daukar ma’aikata.
A karshe, majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi domin kiran shugaban SUBEB ya bayyana tare da kare tsarin daukar aikin.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
