Connect with us

Ilimi

NELFUND Ya Raba Sama da Naira Biliyan 3 ga Daliban BUK

Published

on

Daga Khadijah Aliyu

Asusun Bada Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya raba jimillar Naira Biliyan 3 da Miliyan 39 a matsayin kudaden karatu ga daliban Jami’ar Bayero da ke Kano su  27,640,  a wani  mataki na fadada damar samun ilimi cikin sauki.

Shugaban Jami’ar, Haruna Musa ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da Darakta Janar na NELFUND, Akintunde Sawyerr, tare da tawagarsa suka kai jami’ar.

Ziyarar, na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da kuma tattauna batutuwan da suka shafi kudaden da ke bai wa dalibai.

A jawabinsa, Farfesa Haruna Musa ya yaba wa NELFUND kan irin tasirinsa ga dalibai, yana mai cewa shirin ya taimaka matuka wajen kara damar shiga makarantu ga dimbin ‘yan Najeriya da ba za su iya yin rajista ba a baya.

Ya ce a zangon karatu na shekarar 2023/2024, daliba BUK 113 ne suka ci gajiyar shirin, inda aka biya Naira Biliyan 1 da Miliyan 494 a matsayin kudaden karatu.

Ya kara da cewa adadin ya karu sosai a zangon 2024/2025 zuwa dalibai 14,539, wanda kudaden suka kai jimillar Naira Biliyan 1 da Miliyan 545.

“Gaba daya, jimillar dalibai 27,640 daga Jami’ar Bayero sun amfana da shirin NELFUND, inda kudaden makaranta suka kai Naira Biliyan 3 da Miliyan 39, baya ga kudaden amfanin yau da kullum da ake biya kai tsaye ga daliban,” in ji shi.

Sai dai Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa wasu dalibai sun fuskanci matsaloli yayin neman lamunin da kuma karbar kudade ta shafin NELFUND. Inda ya bayyana fatan tawagar za ta zage damtse wajen tabbatar da magance wadannan matsaloli.

Tun da farko, Mista Sawyerr ya ce ziyarar na da nufin  kara zurfafa hadin gwiwa ne da jami’ar, yana mai tabbatar da cewa za a duba korafe-korafen dalibai domin saukaka tsarin neman lamunin da sake nema.

Haka kuma ya shawarci jami’ar da ta rika bude shafinta a kan lokaci domin bai wa dalibai damar yin rajista da wuri, tare da samun kudaden amfanin yau da kullum ba tare da jinkiri ba.

Labarai

Labarai14 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai18 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara