Labarai
Shugaba Tinubu Ya Mika Sakon Ta’aziyya ga Iyalan Tsohon Shugaban INEC Attahiru Jega
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga Farfesa Attahiru Jega, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Bunƙasa Harkokin Kiwo, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza Jega.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaban ya bayyana marigayiyar Hadiza Jega a matsayin mace jajirtatta, wacce ta kasance ginshiƙi ga mijinta a tsawon shekarunsa na hidimtawa kasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Shugaban Ƙasa yayin Sallar jana’izar marigayiyar da aka gudanar a babban masallacin Juma’a da ke Abuja, inda ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasar ga Farfesa Jega da iyalansa.
Tinubu ya kuma yaba da gudunmawar marigayiyar Hadiza Jega ga ilimi da ci gaban al’umma, yana mai jaddada irin tasirin alherinta ga jama’a.
Ya yi addu’ar Allah Ya jikanta da rahama, tare fatan bai wa iyalanta haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
