Connect with us

Labarai

Kungiyar NUJ Reshen Rediyo Najeriya Kaduna ta Taya FRCN Murnar Cika Shekaru 75 da Kafuwa

Published

on

Daga Yusuf Zubairu 

Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Kasa NUJ, reshen Rediyo Najeriya Kaduna ta taya mahukunta da ma’aikatan Rediyon Tarayya(FRCN) murnar cika shekaru 75 da kafuwa.

A cikin wata sanarwa da Shugabanta, Umar Adamu Sarkinfada ya fitar, kungiyar ta bayyana wannan gagarumar nasara a matsayin shaida ta jajircewa, ƙwazo da kuma muhimmiyar gudunmawar da FRCN ke bayarwa wajen ci gaban ƙasa, haɗin kan al’umma da kuma yada sahihan labarai a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Shugaban ya ce, tsawon sama da shekaru saba’in, Rediyon Tarayya na ci gaba da kasancewa amintacciyar murya wajen wayar da kai, ilmantarwa da kuma nishadantar da al’umma, tare da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida masu inganci.

Ya yaba wa ma’aikatan kafar yada labaran bisa jajircewarsu, aiki tuƙuru da sadaukarwa wajen inganta haɗin kan ƙasa da kuma bai wa al’ummomi daban-daban damar a ji ra’ayoyinsu a faɗin ƙasar.

Yayin da yake taya su murna kan wannan nasara, Sarkinfada ya buƙaci mahukunta da su mayar da hankali kan jin daɗin ma’aikata, yana mai jaddada cewa ƙwararrun ma’aikata masu ƙwazo su ne ginshiƙin ci gaba a kowace ma’aikata.

Haka kuma, ya yi kira da a faɗaɗa ayyukan gyaran da ake yi a hedikwatar gidan rediyon zuwa dukkan tashoshin yankuna, domin samar da ingantaccen muhalli na aiki.

Umar Adamu Sarkinfada ya kuma ƙarfafa gwiwar ci gaba da kawo sabbin hanyoyi da kuma bin ƙa’idoji da manufofin da suka gina Rediyon Tarayya tsawon shekaru.

 

Kungiyar NUJ ta yi wa kafar fatan ƙarin shekaru masu albarka, ci gaba da nasara a ayyukanta.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara