Labarai
Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin Najeriya, waɗanda suka jikkata a bakin aiki, da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu yayin hidima ga ƙasa.
Shugaban ya bayyana wannan shiri ne a ranar Lahadi, a yayin da yake bikin cika shekaru 74 da haihuwarsa, domin girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar da jami’an soji ke yi wa ƙasa.
Bola Ahmed Tinubu ya umarci Akanta-Janar na Tarayya da ya buɗe wani asusu na musamman domin wannan shiri, wanda zai rika bayar da tallafi ga sojojin da suka jikkata, da kuma zawarawa, mazajen da matansu suka rasu, da ’ya’yan waɗanda suka mutu yayin hidimar ƙasa.
A matsayin gudunmawar sa ta kai tsaye, shugaban ya yi alƙawarin bayar da dukkan albashinsa tun bayan hawansa mulki a matsayin jarin farko na asusun, domin nuna aniyarsa na tabbatar da cewa ba a manta da waɗanda suka sadaukar da kansu domin zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi, ’yan majalisar dokoki ta ƙasa, kamfanoni masu zaman kansu, abokansa da masu fatan alheri da su mara wa wannan shiri baya, yana mai cewa za a bayyana cikakkun bayanai game da asusun nan gaba kaɗan.
Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa wannan shiri ya samo asali ne daga nauyin da ke kan ƙasa na kula da waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa, da kuma iyalansu da ke ɗaukar nauyin wannan sadaukarwa, ba tare da la’akari da shirye-shiryen inshora da ake da su ba.
Ya ƙara da cewa tallafa wa jami’an soji da iyalansu ba sadaka ba ce, illa wata wajibci ce da ya kamata kowa ya cika.
Shugaban ya kuma sake jaddada kudurin gwamnatinsa na ƙarfafa jin daɗin rayuwar jami’an soji, tare da tabbatar da cewa ana girmama hidimarsu ga ƙasa ta hanyar kulawa mai ɗorewa.
Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
