Labarai
Gwamna Lawal Ya Buƙaci Masu Son Tsayawa Takara Su Aje Mukamansu
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya umurci dukkan ‘yan majalisar zartaswar jihar da ke son takara a zaben shekarar 2027 da su ajiye mukamansu.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar a Gidan Gwamnati, Gusau.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, wannan umarni ya yi daidai da dokar zabe wacce Shugaban kasa ya rattaba hannu a kai, da kuma jadawalin zaben 2027 da hukumar zabe ta kasa INEC ta fitar.
“Yau ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na 64, inda aka tattauna muhimman batutuwa domin ci gaban Jihar Zamfara.

“A jawabin bude zaman taron, gwamnan ya umurci dukkan mambobin majalisar zartarwar da ke neman mukaman siyasa su ajiye aikinsu kafin ko a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2026.”
Sanarwar ta ce, gwamnan ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar, da ya fitar da wata sanarwa ga dukkan jami’an gwamnati da ke da burin takara, wanda zai bukaci su ajiye mukamansu kafin ranar da aka kayyade.

Haka kuma, an umarci Shugaban Ma’aikata da ya aikawa dukkan ma’aikatan gwamnati da ke da niyyar yin takara domin su ajiye aikinsu.
Gwamna Lawal ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen hidimar al’ummar Jihar Zamfara.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
