Labarai
Gwamna AbdulRazaq, Saraki da Sarkin Ilorin Sun Taya Musulmi Murnar Sallah
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, tare da Sanata Abubakar Bukola Saraki da Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, sun taya al’ummar Musulmi murnar bikin Eid-el-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya roƙi Allah da Ya karɓi ibadun da aka yi da addu’o’in da aka gabatar a tsawon watan Ramadan, tare da roƙonSa da Ya ba wa bayinsa ikon ci gaba da kasancewa masu biyayya da ƙasƙantar da kai gare Shi.
Haka kuma ya buƙaci Musulmi da su ci gaba da riko da kyawawan halaye da watan Ramadan ya koyar, tare da kiyaye umarnin Allah a kowane lokaci.
Shi ma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, a cikin wata sanarwa da jami’in sa kan harkokin cikin gida, Abdulganiyu Abdulqadir ya fitar, ya taya Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su ci gaba da kasancewa masu fata da haɗin kai duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
A nasa ɓangaren, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, cikin saƙon da mai magana da yawunsa, Abdulazeez Arowona ya fitar, ya taya daukacin al’ummar Musulmi a Daular Ilorin da Jihar Kwara da ma ƙasar Najeriya baki ɗaya murnar kammala azumin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijira (2026 Miladiyya).
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
