Labarai
An Bukaci Musulmi Su Yi Amfani da Darussan Ramadan — Janar Abdulsalami
Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya buƙaci al’ummar Musulmi da su aiwatar da darussan da suka koya a watan Ramadan domin inganta rayuwarsu.
Janar Abdulsalami ya yi wannan kira ne bayan gudanar da sallar Idi raka’o’i biyu ta Eid-el-Fitr a filin sallar Idi na Minna, Jihar Neja.
Ya kuma ƙara da cewa ya kamata Musulmi su ci gaba da taimakon juna tare da nuna ƙauna da jin ƙai ga marasa galihu, bisa koyarwar addinin Musulunci.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da gargaɗin matasa a jihar da su kasance masu natsuwa, su guji duk wani abu da zai iya tayar da tarzoma yayin bikin Sallah.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba, wanda ya wakilce shi, ya ce gwamnan yana cikin gari, kuma daga bisani zai je fadar Sarkin Minna, Dakta Umar Faruk Bahago, domin halartar bikin durbar.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, ya tunatar da Musulmi cewa daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, azumi ne kaɗai Allah Ya ce nasa ne kai tsaye, kuma Shi ne zai ba da lada ga duk wanda ya yi shi yadda ya kamata.
Sai dai ya buƙaci Musulmi da su bayar da Zakatul Fitr ga masu buƙata domin su samu abin da za su ciyar da iyalansu a ranar Sallah.
Aliyu Lawal/ Minna
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
