Labarai
Mukaddashin Gwamnan Zamfara Ya Taya Musulmi Murnar Sallah
Mukaddashin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mummuni, ya taya al’ummar Musulmi a fadin jihar murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bikin Eid-el-Fitr.
A cikin sakon Sallah da ya gabatar a madadin Gwamnan Jihar, Dakta Dauda Lawal, mukaddashin gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya karɓi ibadun da aka yi a watan Ramadan, Ya gafarta kura-kurai, tare da bai wa Musulmi rahama da ‘yanci.
Mani Malam Mummuni ya bayyana Eid-el-Fitr a matsayin lokaci na godiya da nazari, inda ya buƙaci al’ummar jihar Zamfara da su gudanar da bukukuwan cikin lumana da bin doka da oda.
Ya kuma ja hankalin matasa da yara da su kasance masu ɗa’a da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah.
Mukaddashin gwamnan ya kuma yi addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu a wannan lokaci, yana roƙon Allah da Ya gafarta musu tare da ba su aljanna.
Ya nuna godiya ga al’ummar jihar bisa ci gaba da yi wa gwamnati addu’a, yana mai cewa ingantuwar tsaro da ake samu a halin yanzu na da alaƙa da haɗin kai da kuma addu’o’in jama’a tare da haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
Mani Mummuni ya buƙaci a ci gaba da yin addu’a da goyon baya, tare da ƙarfafa al’umma su ci gaba da aiki tare da gwamnati domin shawo kan sauran ƙalubalen tsaro da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Dangane da harkokin siyasa, mukaddashin gwamnan ya bayyana cewa matakin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka na shiga jam’iyyar APC an yi shi ne domin amfanin jihar, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen inganta tsaro da hanzarta ci gaba.
Ya ƙara da cewa jihar Zamfara na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a ƙarƙashin wannan gwamnati, tare da jaddada kudurin gwamnati na aiwatar da ƙarin ayyukan ci gaba.
A ƙarshe, ya buƙaci al’ummar Zamfara da su ci gaba da bai wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal goyon baya domin kai jihar ga matakin ci gaba da wadata.
Mukaddashin gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati na mai da hankali wajen ganin Zamfara ta yi gogayya da sauran jihohi a fannin ci gaba da ingantaccen hidima ga jama’a.
Ya yi wa dukkan Musulmi fatan gudanar da bikin Eid-el-Fitr cikin kwanciyar hankali da farin ciki.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
