Connect with us

Labarai

Kungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Wata ƙungiyar al’umma mai suna Hadejia Advocacy ta yaba wa Gwamnan  Jigawa, Umar Namadi, kan yadda ya shiga tsakani a lamarin Walida wadda ake zargin wani jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) mai suna Ifeanyi Festus Onyewuenyi da yin garkuwa da ita.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ceto yarinyar tare da jaririnta, waɗanda yanzu suke ƙarƙashin kulawar Gwamnatin Jihar Jigawa, wata babbar shaida ce da ke nuna ƙudirin Gwamna Namadi na kare rayuwa, mutunci da walwalar al’ummar jihar.

Shugaban ƙungiyar, Comrade Abubakar Babangida ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani gangamin zanga-zangar goyon baya da aka gudanar a  garin Hadejia.

Comrade Abubakar ya sake jaddada kudirin ƙungiyarsu na ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Namadi baya domin ganin an bi wannan shari’a har zuwa ƙarshe, tare da tabbatar da an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.

Sai dai masu zanga-zangar lumanar sun soki zanga-zangar da ƙungiyar ‘Hadejia Ina Mafita’ ta shirya, inda suka bayyana ta a matsayin wadda ke yaɗa bayanai marasa sahihanci da kuma ruɗar da jama’a, lamarin da ka iya haifar da rikici da hargitsi a cikin al’umma.

Sun kuma yi kira ga shugabannin Hadejia Ina Mafita da su riƙa yin taka-tsantsan yayin da suke magana ko sharhi kan irin waɗannan muhimman batutuwa, tare da gujewa siyasantar da su ko kuma ɓata sunan gwamnati.

Hakazalika, wata ƙungiyar mata mai suna Jigawa Women Development Initiative ta gudanar da zanga-zangar lumana a Dutse, babban birnin jihar, domin nuna farin cikinsu kan rawar da Gwamna Namadi ya taka a matsayin uba da jagora a lamarin Walida Abdullahi.

Ƙungiyar matan ta bayyana matuƙar damuwarta kan abin da ya faru, tare da nuna tausayi ga wadda abin ya shafa da iyayenta bisa irin mummunan cin zarafin da ake zargin wanda ake tuhuma ya yi mata.

Don haka sun yi kira ga al’umma gaba ɗaya da su haɗa kai wajen nuna goyon baya ga Gwamnatin Jihar Jigawa domin tabbatar da cewa an yi adalci ga Walida Abdullahi.

Labarai

Labarai16 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai19 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara