Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara yin kira ga ‘yan kwangilar da aka baiwa sayen kayan abincin shan ruwa da su sanya tsoron Allah wajen sayen kayayyakin abinci masu inganci.

Shugaban kwamitin ciyarwar  na watan Ramadan kuma Kwamishinan ma’aikatar ilimi matakin farko na jihar Dr Lawan Yunusa Danzomo ya yi wannan kiran a lokacin da ya ziyarci wasu cibiyoyin dafa abincin a yankin karamar hukumar Birnin kudu.

Ya bukace su da su sanya tsoron Allah wajen sayen kayayyakin abinci masu inganci da kuma tsafta kamar yadda aka cimma yarjejeniya da su da gwamnatin jihar.

Ya nuna gamsuwar sa dangane da yadda ake dafawa da raba abincin buda baki a cibiyoyin da aka tanadar a garuruwan Birnin Kudu da Kantoga da Kafin gana da Kangire dake karamar hukumar Birnin Kudu.

Dr Lawan Yunusa Danzomo wanda ya ziyarci cibiyoyin don ganewa idon sa yanda yawan abincin da tsaftarsa ya ke, ya nuna gamsuwarsa dangane da yadda wadanda aka baiwa alhakin aikin suke gudanar da rabon.

Yace Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Malam Umar Namadi ta bullo da shirin ciyarwar ne da nufin tallafawa dukkanin al’ummar jihar Jigawa musamman masu karamin karfi don su sami abin da za su yi buda baki da shi a lokacin shan ruwa.

A don haka, Dan Zomo ya yi kira ga yan kwangilar da su tabbatar suna sayen kayan abincin a yankunan da za a dafa  don a karfafi tattalin arzikin al’ummar yankunan.

Yayi nuni da cewar, a kowacce cibiya ana dafa shinkafa da kunun tsamiya da kosai don rabawa mabukata har na tsawon watan Ramadan.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa Gwamnati addu’oi ra musamman a wannan watan na Ramadan domin samun nasarar gudanar da aiyukan alherin da kuma zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar Jigawa.

A jawaban su daban-daban, al’ummar garuruwan da kwamishinan ya ziyarta sun godewa gwamnatin jihar bisa bullo da shirin ciyarwar.

Sun kuma yi addu’ar fatan alkhairi ga Gwamna Umar Namadi da gwamnatin sa da ma jihar jigawa baki daya.

 

Labarai

Labarai22 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara