Labarai
Wani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
Daga Aminu Dalhatu
Wani bam kirar hannu ya fashe a kan hanyar Gusau zuwa Funtua, inda ya shafi wata babbar mota da ke dauke da siminti daga Jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa bam din ya fashe ne da sanyin safiyar yau Laraba a Unguwar Maichida.
Motar ta samu mummunar illa, lamarin da ya haifar da tsaiko ga masu ababen hawa a kan hanyar.

Majiyoyin yankin sun ce ana zargin ‘yan bindiga ne suka dasa bam din, wanda ya tashi a daidai lokacin da tirelar ke wucewa ta wurin.
An ce fashewar ta lalata gaban motar sosai, wadda ke kan hanyarta ta zuwa Kaduna daga Sokoto, amma ba a samu asarar rai ba, yayin da aka ceto direban da ransa.

Wani mazaunin yankin da ya yi magana ta waya ya ce fashewar ta faru ne ‘yan sa’o’i kaɗan bayan wata haɗakar jami’an ‘yan sanda da sojoji ta sake buɗe hanyar Kucheri zuwa Danjibga zuwa Keta a ƙaramar hukumar Tsafe, wadda ta kasance a rufe sama da wata guda.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da bincike game da hakan.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
