Labarai
Zamfara Ta Yi Allah-wadai da Harin Ta’addanci Anka
Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kakkausar Allah-wadai da harin ‘yan bindiga na ta’addanci da aka kai ƙauyen Dutsin Dan-Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 50, da jikkatar da dama, tare da lalata dukiyoyi da raba mutane da muhallansu.
Ƙauyen Dutsin Dan-Ajiya, wanda ke da nisa da hanyoyi marasa kyau, ya fuskanci mummunar barna yayin da ‘yan bindigar suka ƙona fiye da rabin ƙauyen, tare da yin awon gaba da mata da yara da dama.
Yayin da yake jagorantar tawagar gwamnati zuwa yankin, Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mumini, ya bayyana harin a matsayin na rashin imani da rashin tausayi, tare da cewa laifi ne kan bayin Allah marasa laifi.
Mataimakin gwamnan, wanda ya jajanta wa al’ummar yankin a madadin gwamnati da al’ummar jihar, ya buƙaci mazauna yankin da su yi haƙuri da juriya, yana mai cewa wannan jarabawa ce daga Allah wadda za ta iya samun kowa, tare da ƙarfafa musu gwiwar su dogara ga Allah a wannan lokaci mai wahala.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin hukumomin tsaro na tarayya da ke aiki a jihar, amma ya nuna damuwa kan rashin zuwan wata tawaga daga gwamnatin tarayya domin jajanta wa gwamnatin da al’ummar Zamfara kan irin waɗannan hare-hare.
Ya jaddada cewa nuna haɗin kan ƙasa a irin waɗannan lokuta yana da muhimmanci domin tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa rayuwar kowane ɗan Nijeriya na da matuƙar daraja.
Mataimakin gwamnan ya tabbatar da mutuwar sama da mutum 50 yayin jawabinsa a fadar Sarkin Anka. Ya kuma sake nanata aniyar gwamnati na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da jami’an tsaron tarayya, zuba jari da kayan aiki da dabarun tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri, da kuma tallafa wa tsare-tsaren tsaro na al’umma cikin bin doka.
A matsayin matakin gaggawa na tallafi, ya sanar da bayar da naira miliyan 23, buhuna 200 na hatsi, da kuma sutura 200 na maza da na mata domin rabawa ga waɗanda abin ya shafa. Haka kuma ya bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin daidaita al’amura da hana sake aukuwar hare-hare.
Tun da farko, Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, ya bayyana harin a matsayin na biyu mafi muni a tarihin Ƙaramar Hukumar Anka. A cewarsa, kusan ƙauyuka 60 a Anka kaɗai sun zama kufai ko kuma an raba al’ummarsu da muhallansu tun bayan fara matsalar ‘yan bindiga.
A nasa jawabin, Hakimin Dutsin Dan-Ajiya, Mohammed Junaidu, ya roƙi gwamnatin jihar da ta magance ƙarancin jami’an tsaro a yankin, yana mai cewa ƙauyuka da dama a kusa sun rasa mazauna sakamakon hare-haren da ake kai musu akai-akai.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana, inda suka fara harbe-harbe da ƙona gidaje, lamarin da ya ɗauki sama da sa’o’i biyu.
“Mun binne mutane 33, yayin da wasu suka ƙone har ba a gane su ba. An kuma lalata gidaje da rumbunan hatsi,” in ji shi.
Wakilinmu da ya ziyarci yankin tare da tawagar Mataimakin Gwamna ya ruwaito cewa al’ummar yankin na cikin tsananin buƙatar tallafin gwamnati, musamman a ɓangaren samar da muhimman abubuwan more rayuwa.
Hakazalika, a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya miƙa motocin yaƙi masu sulke (APCs) da jirage marasa matuƙi (drones) ga sojojin Nigeria a matsayin wani ɓangare na ƙudirin gwamnatin jihar na tunkarar matsalar ‘yan bindiga da muhimmanci.
COV/AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
