Kasuwanci
‘Yan Sandan Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.
A cewar sanarwar, ba tare da bata lokaci ba, tawagar jami’an tsaro ta fara gudanar da wani bincike na hadin gwiwa, wanda ya kai ga ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, yayin da mutanen da aka ceto suka koma ga iyalansu.
Ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya yabawa ‘yan sandan bisa gaggauwa da daukar matakin da suka dauka.
Ya nanata kwazon rundunar tare da sauran jami’an tsaro na ganin an ceto duk wadanda aka sace tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
CP Maikaba ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da ba su gane ba ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin kawo dauki cikin gaggawa.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta wargaza maboyar barayi da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
REL/AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
