Labarai
Dimbin Jama’a Sun Fito Yayin Fara Taron Gunduma na APC
’Yan jam’iyyar APC a Jihar Kwara sun fito da yawa domin halartar fara Taron Gunduma (Ward Congress) na jam’iyyar da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar.
Daga yankunan Adewole, Oju Ekun Zarumi da Alanamu a Ilorin ta Yamma, zuwa Ibagun a Ilorin ta Gabas, Alapa a Asa, Share a Ifelodun, da Okuta a Baruten, da sauran wurare, mambobin jam’iyyar sun halarta da dimbin yawa domin shiga cikin shirin.
Jam’iyyar ta amince da amfani da tsarin tabbatarwa (affirmation) wajen mayar da mafi yawan shugabannin jam’iyya masu ci a kan mukamansu, bisa la’akari da kwazon da suka nuna a aikinsu — sai dai a wasu wurare kalilan inda tsarin rabon mukamai (zoning) da wasu dalilai na musamman suka dauki hankalin al’amura.
Wakilan hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ne ke sa ido kan yadda ake gudanar da taron.
A nasa jawabin, Shugaban APC na Jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya yaba wa mambobi da shugabannin jam’iyyar bisa goyon baya, hadin kai, da kuma yadda suka nuna da’a da zaman lafiya yayin fara taron gundumar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
