Connect with us

Labarai

Zamfara Na Neman Karin Hadin Gwiwa Domin Magance Matsalar Yara Marasa Zuwa Makaranta

Published

on

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa da abokan hulda na ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da hadaddiyar tawaga daga shirin ciyarwa ga dalibai a Shirin Abinci na Malaisar dinkin Duniya da cibiyar nazarin harkokin abinci ta duniya.

A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai a Ofishin SSG, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, SSG ya bayyana ilimi a matsayin babbar fifiko ga gwamnatin Gwamna Dauda Lawal, yana mai cewa gwamnati ta dauki kwararan matakai domin gyara sakacin da aka yi wa bangaren ilimi tsawon shekaru.

Nakwada ya bayyana cewa bayan ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi da gwamnatin yanzu ta yi, an gyara tare da samar da kayan koyarwa da na koyo a kusan makarantu 600 a fadin jihar.

Ya sake jaddada kudurin gwamnati na kara yawan shigar yara makaranta, da tabbatar da dorewarsu a makaranta har su kammala karatu, yana mai nuni da cewa shirin ciyar da dalibai a makaranta na daya daga cikin muhimman hanyoyin karfafa musu gwiwa su ci gaba da zama a aji.

Ya ce, “Ya kasance babban kalubale a rike yara a makaranta ba tare da samar musu da abinci ba. Wannan bangare ne da muke bukatar karin hadin gwiwa da tallafi.”

Ya kara da cewa, “Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa babu wani yaro da za a bari a baya a tsarin ilimi. Da matakan da muka dauka a yanzu, muna da yakinin cewa za a samu raguwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara.”

Bisa kididdigar da Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Zamfara (ZSUBEB) da UNICEF suka bayar, jihar ta samu kimanin yara 455,947 da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2025, wanda ke nuna raguwar kaso 48.4 cikin dari idan aka kwatanta da adadin 883,953 da hukumar ilimi bai daya ta kasa  ta fitar a shekarar 2022.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan ci gaba ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen da aka ci gaba da aiwatarwa a bangaren ilimi karkashin gwamnatin Lawal.

SSG ya tuna cewa a watan Yulin 2025, Gwamna Lawal ya kaddamar da shirin ciyar da dalibai a makaranta tare da hadin gwiwar Cibiyar Bunƙasa Tattalin Arziki ta Kasa da Kasa da kuma FINPACT Development Foundation, inda aka fara da dalibai kimanin 4,300 a makarantu na gwaji a fadin jihar. An tsara shirin ne domin kara yawan shigar yara makaranta, rage ficewarsu, da kuma rage yawan yaran da ke yawo a tituna.

A nata bangaren, Mataimakiyar Shugabar Shirye-shirye ta WFP a Nijeriya, Darline Raphael, ta yaba wa Gwamna Lawal bisa bai wa ilimi muhimmanci, musamman ilimin ‘ya’ya mata. Ta bayyana kwarin gwiwarta cewa da irin wannan jajircewa ta siyasa da gwamnatin jihar ta nuna, nan gaba kadan Zamfara za ta zama abin koyi a fannin aiwatar da shirye-shiryen ciyar da dalibai a makaranta a Nijeriya.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara