Connect with us

Labarai

Majalisar Kasa Ta Amince Da Ba Hukumomin Tsaro Ikon Gudanarda Aikin su

Published

on

Majalisar Dattawa ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da bai wa Hukumar Tsaro da Leken Asiri ta Kasa cikakken goyon baya domin ta gudanar da aikinta yadda ya kamata, bisa kundin tsarin mulki, wajen kare kasa da al’ummarta.

 

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaro da Leken Asiri, Sanata Yahya Abdullahi, ne ya bayyana hakan a jawabinsa yayin zaman kare kasafin kudi da aka gudanar a wannan Laraba.

 

Ya bayyana cewa aikin kasafin kudin na bana yana da matukar muhimmanci, duba da irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu. Ya ce suna sane da sarkakiyar matsalar tsaro da ke gaban kasa, wadda ke bukatar hadin kan kowa da kowa domin magance ta.

 

Ya kara da cewa a baya-bayan nan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro, kuma domin tabbatar da wannan mataki na shugaban kasa, kwamitin ya ga ya dace a daidaita kasafin kudin da ake ware wa hukumomin leken asiri daidai da girman kalubalen da ake fuskanta.

 

Ya ce, “Domin hukumomin tsaro su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata tare da tinkarar karuwar barazanar tsaro da ke barazana ga zaman lafiyar kasa, wajibi ne a samar musu da isasshen kudade.”

 

Sai dai ya tabbatar da cewa a matsayinsu na kwamitin, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen karfafa hukumomin da ke karkashinsu, domin su zama masu karfi da kuma saurin daukar mataki kan duk wata barazanar tsaro da leken asiri da ke fuskantar kasar nan.

 

A nasa jawabin na bude taro, Babban Sakataren Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Muhammad Sanusi, wanda ya wakilci Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana manyan bangarorin da Hukumar Leken Asiri za ta fi mayar da hankali a shekarar kasafin kudi ta 2026.

 

Ya ce daga cikin abubuwan da za su fi mayar da hankali a kai akwai yaki da ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane ta hanyar karfafa ayyukan leken asiri da dabarun hadin gwiwa da al’umma. Haka kuma za su mayar da hankali wajen kare muhimman ababen more rayuwa domin tabbatar da tsaron tattalin arziki da wadatar abinci, tare da inganta tsaron muhimman kayayyakin mai da iskar gas domin kara yawan samar da mai.

Ya kuma bayyana cewa za su mai da hankali kan tsaron teku da iyakoki, inganta tsaron yanar gizo (cyber security), da kuma ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a dukkan yankunan rundunonin tsaro uku da ma kasa baki daya.

 

Muhammad Sanusi ya kara da cewa suna shirin inganta horo da kara kwarewar ma’aikata da tura su yadda ya kamata domin tinkarar sabbin kalubalen tsaro, ciki har da tasirin rikice-rikicen siyasa a kasashen yammacin Afirka makwabta.

 

Ya kuma ce shekarar kasafin kudi ta 2025 na tafiya ne tare da wasu kalubale, inda daga ciki akwai tsarin kasafin kudi na “envelope” wanda ke takaita yadda ake rabon albarkatu, da kuma jinkirin sakin kudaden tafiyar da ofisoshi (overhead cost), da rashin aiwatar da sakin bangaren kudaden ayyukan manyan ayyuka (capital) na shekarar 2025.

 

Haka kuma akwai matsalar jinkirin sakin kudaden ma’aikatan ofisoshin kasashen waje, gibin alaka da wasu kudade na shekarar 2024, da kuma rashin sakin wasu kudaden manyan ayyuka gaba daya.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara