Ilimi
SUBEB da UNICEF Sun Horas da Malaman Firamare a Jigawa
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Jigawa (SUBEB), tare da haɗin gwiwar Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta horas da malamai kan yadda za su gudanar da gwajin karatu da lissafi ga ɗaliban makarantun firamare.
Mai bada shawara kan tantance ilimin yara a matakin farko na UNICEF Dakta Farouk Aliyu, ya bayyana cewa horon na kwanaki huɗu wanda ya fara a ranar Litinin, na da nufin tantance matsayin yadda dalibai ke koyon karatu a makarantu.

A cewarsa, sun mayar da hankali ne kan ɗaliban aji ɗaya da aji biyu na firamare da kuma malamansu a fannin lissafi da harshen Hausa a kowace makaranta.
Dakta Farouk Aliyu ya ce manufar wannan shiri ita ce samar da hanya mafi sauki da dalibai za su samu ƙwarewar karatu da lissafi a matakin farko a Jihar Jigawa.

Ya ƙara da cewa, ana kuma son fahimtar yadda malamai ke koyarwa tare da tantance ko suna bin hanyoyin koyarwa da UNICEF da sauran hukumomin ilimi suka koyar.
Ya ce idan aka samu gibi, hakan zai sa a sake horas da malamai da tsara manufofi, ko ma sauya tsarin manhajar karatu gaba ɗaya.

Mashawarcin na UNICEF ya ce an horas da mahalarta 67 waɗanda za su tattara sahihan bayanai masu inganci da za su taimaka wajen tsara manufofin da za su tallafa wa tsarin ilimi a jihar.
UNICEF ta dade tana tallafa wa tsarin ilimi a Jigawa da Najeriya baki ɗaya ta hanyar horas da malamai da samar da kayayyakin koyo da koyarwa.

Wannan horon ya ƙara jaddada ƙudirin Kungiyar Tarayyar Turai da gwamnatin Jihar Jigawa wajen inganta sakamakon koyo tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ƙwarewar karatu da lissafi tun daga tushe.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, an horas da sama da malamai 1,680 na azuzuwan firamare daya zuwa uku, kan hanyoyin koyar da karatu da lissafi domin inganta koyarwa da samun sakamako mai kyau.

Haka kuma, an raba sama da kayayyakin koyo da koyarwa 152,386 ga ɗaliban matakin farko a makarantun da shirin ya shafa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
