Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jigawa Ta yi Tanadin Abinci na Musamman ga Masu Lalura
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa za ta ci gaba da samar da abinci da musamman ga Alhazan jihar da ke da matsalar hawan jini da ciwon sukari a yayin aikin Hajjin shekarar 2026.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar gwajin lafiya a Asibitin Gwamnati na Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, hukumar ta dade tana samar da wannan abinci na musamman ga Alhazan jihar a matsayin wani mataki na inganta lafiya da walwalar su.
Ya kara da cewa, hukumar na bai wa lafiya da walwalar kowanne Alhaji muhimmanci sosai, tare da bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burin da aka sanya a gaba.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, an kuma tsara shirin bayar da abinci sau uku ga Alhazan jihar a kasar Saudiyya.
A yayin da yake yin sharhi kan gwajin lafiya, shugaban hukumar ya ce mataki na hudu na gwajin yana tafiya cikin nasara bisa yadda Maniyyatan ke bada hadin kai.

Saboda haka, ya jaddada cewa hukumar ta himmatu himma wajen daukar nauyin kudaden gwajin lafiya, wanda kyauta ne ga dukkan Maniyyatan jihar.
Haka kuma, jagoran ƙungiyar likitoci, Dr. Abubakar Habib, ya tabbatar da kudurinsu na gudanar da gwajin lafiya bisa ka’idojin hukumar kula da Alhazan jihar da kuma hukumomin Hajj da Umrah na Saudiyya.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
